Fiye da mutum miliyan 1.9 ne suka nemi aikin shiga cikin Hukumar Tsaro ta Fararen Hula (Civil Defence), Hukumar Shige da Fice (Immigration), Hukumar Gyaran Hali (Correctional Service), da kuma Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (Federal Fire Service).
Rahotanni sun nuna cewa daga cikin wannan adadi, mutum dubu 30 ne kawai za a dauka aiki.
Dangane da yadda masu neman aikin suka rabu, Jihar Kogi ce ke da mafi yawan masu nema, inda suka kai fiye da mutum 116,000.
Haka zalika, Jihar Kaduna na da fiye da mutum 114,000, Benue na da mutum 110,000 yayin da Jihar Kano ke da fiye da mutum 89,000.
Rahoton ya kuma nuna cewa Jihar Katsina na da fiye da mutum 76,000, yayin da Jihar Nasarawa da Oyo suka haura mutum 67,000 kowannensu.
Sannan, Jihar Kebbi da Jigawa suna da mutum 34,000 da 44,000 bi da bi.
Baya ga haka, Babban Birnin Tarayya Abuja na da fiye da mutum 30,000 da suka nemi aikin, yayin da Jihar Legas ta yi rajistar mutum fiye da 14,000.
Sai dai jihar da ta fi kankanta wajen yawan masu neman aikin ita ce Jihar Bayelsa, inda mutum 11,669 ne kacal suka nemi aiki a cikin wadannan hukumomin tsaron.

Comments
Post a Comment