Majalissar Dokokin Jihar Katsina Ta Nemi A Ɗauki Matakan Gaggawa Kan Matsalar Tsaro A Matazu Da Sabuwa
Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta yi kira ga Gwamnatin Jiha da ta Tarayya da su ɗauki matakan gaggawa kan ƙara ta’azzarar matsalar tsaro a Matazu, Sabuwa da wasu yankuna.
A zaman majalisar na ranar Litinin 11/08/2025, ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, Majalisar ta amince da ƙudurin ƙara yawan jami’an tsaro, musamman a Tashar Bawa da sauran wuraren da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga.
Ƙudurin ya fito ne daga Hon. Ibrahim Umar Dikko na Matazu da Hon. Ibrahim Danjuma Machika na Sabuwa, inda suka nuna damuwa kan kashe-kashe, barin gidaje da hana manoma noma sakamakon harin ƴan fashin Daji. Sun kuma nuna damuwa da janyewar jami’an tsaro daga wasu ƙauyuka.
‘Yan majalisa daga wasu mazaɓu sun goyi bayan ƙudurin tare da buƙatar a dawo da jami’an tsaro da inganta haɗin gwiwa don dawo da zaman lafiya.
Shugaban Majalisar ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyi a duk faɗin jihar.

Comments
Post a Comment