A Zeno.FM Station Ƴan Nijeriya 69,376 ne su ka cike matakin farko na rijistar katin zaɓe ta yanar-gizo a awanni 7 da buɗe shafin - INEC Skip to main content

Burkina Faso da Mali sun ƙaurace wa taron hafsoshin soji na Afirka da ke gudana a Najeriya

 Burkina Faso da Mali sun ƙaurace wa taron hafsoshin soji na Afirka da ke gudana a Najeriya Kasashen Burkina Faso da Mali sun kaurace wa babban taron shugabannin sojojin Afirka da Najeriya ta shirya a Abuja, lamarin da ya nuna rashin jituwar diflomasiyya tsakanin kasashen Sahel masu mulkin soja da makwabtansu. Sai dai Nijar ce kadai daga cikin kasashen Alliance of Sahel States (AES) da ta halarci taron, inda jakadarta mai kula da harkokin tsaro, Colonel Major Soumana Kalkoye, ya wakilta ta. Babban Hafsan Sojin Najeriya, Christopher Musa, ya bukaci sabon tsarin hadin gwiwa na tsaro karkashin jagorancin Afirka, yana mai cewa kalubalen tsaro “ba su da iyaka” kuma dole a fuskance su tare. Najeriya da Nijar sun taba samun sabani bayan juyin mulkin 2023, amma daga baya suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro.  Sai dai janyewar Nijar daga rundunar hadin gwiwa ta yankin ya kawo cikas ga yaki da ’yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi.

Ƴan Nijeriya 69,376 ne su ka cike matakin farko na rijistar katin zaɓe ta yanar-gizo a awanni 7 da buɗe shafin - INEC

 Ƴan Nijeriya 69,376 ne su ka cike matakin farko na rijistar katin zaɓe ta yanar-gizo a awanni 7 da buɗe shafin - INEC

Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa (INEC) ta ce ta samu mutane 69,376 da suka yi rajistar farko ta yanar-gizo cikin awa bakwai kacal tun bayan da ta sake buɗe shafin ci gaba da yin rijistar katin zaɓe a fadin ƙasa.

Kwamishinan INEC na ƙasa, Sam Olumekun, ya ce rajistar ta fara aiki da karfe 8:30 na safe a ranar Litinin, inda zuwa 3:30 na rana aka samu wannan adadi.

 Daga cikin su, maza sun kai 33,803, mata kuma 35,573, yayin da matasa masu shekaru 18 zuwa 34 suka kai sama da kashi 69%.

Ya bayyana cewa rajistar kai tsaye ta mutum za ta fara ranar 25 ga Agusta a ofisoshin INEC 811 a fadin jihohi da kananan hukumomi, daga karfe 9 na safe zuwa 3 na rana a ranakun aiki.

INEC za ta rika fitar da rahoton mako-mako kan yadda ake gudanar da rijistar, ciki har da bayanai kan jihohi, jinsi, shekaru da sana'a.

 Hukumar ta kuma jaddada cewa rajista ta buɗe ne kawai ga ‘yan Najeriya masu shekaru 18 da sama waɗanda ba su taɓa yin rajista ba, yayin da sauya rajista da maye gurbin kati da ya ɓata ko ya lalace.

Comments

Popular posts from this blog

Burkina Faso da Mali sun ƙaurace wa taron hafsoshin soji na Afirka da ke gudana a Najeriya

 Burkina Faso da Mali sun ƙaurace wa taron hafsoshin soji na Afirka da ke gudana a Najeriya Kasashen Burkina Faso da Mali sun kaurace wa babban taron shugabannin sojojin Afirka da Najeriya ta shirya a Abuja, lamarin da ya nuna rashin jituwar diflomasiyya tsakanin kasashen Sahel masu mulkin soja da makwabtansu. Sai dai Nijar ce kadai daga cikin kasashen Alliance of Sahel States (AES) da ta halarci taron, inda jakadarta mai kula da harkokin tsaro, Colonel Major Soumana Kalkoye, ya wakilta ta. Babban Hafsan Sojin Najeriya, Christopher Musa, ya bukaci sabon tsarin hadin gwiwa na tsaro karkashin jagorancin Afirka, yana mai cewa kalubalen tsaro “ba su da iyaka” kuma dole a fuskance su tare. Najeriya da Nijar sun taba samun sabani bayan juyin mulkin 2023, amma daga baya suka rattaba hannu kan yarjejeniyar tsaro.  Sai dai janyewar Nijar daga rundunar hadin gwiwa ta yankin ya kawo cikas ga yaki da ’yan ta’adda a yankin Tafkin Chadi.

Fiye da mutum miliyan 1.9 ne suka nemi aikin shiga cikin Hukumar Tsaro ta Fararen Hula (Civil Defence), Hukumar Shige da Fice (Immigration), Hukumar Gyaran Hali (Correctional Service), da kuma Hukumar Kashe Gobara ta Tarayya (Federal Fire Service).

  Rahotanni sun nuna cewa daga cikin wannan adadi, mutum dubu 30 ne kawai za a dauka aiki. Dangane da yadda masu neman aikin suka rabu, Jihar Kogi ce ke da mafi yawan masu nema, inda suka kai fiye da mutum 116,000. Haka zalika, Jihar Kaduna na da fiye da mutum 114,000, Benue na da mutum 110,000 yayin da Jihar Kano ke da fiye da mutum 89,000. Rahoton ya kuma nuna cewa Jihar Katsina na da fiye da mutum 76,000, yayin da Jihar Nasarawa da Oyo suka haura mutum 67,000 kowannensu. Sannan, Jihar Kebbi da Jigawa suna da mutum 34,000 da 44,000 bi da bi. Baya ga haka, Babban Birnin Tarayya Abuja na da fiye da mutum 30,000 da suka nemi aikin, yayin da Jihar Legas ta yi rajistar mutum fiye da 14,000. Sai dai jihar da ta fi kankanta wajen yawan masu neman aikin ita ce Jihar Bayelsa, inda mutum 11,669 ne kacal suka nemi aiki a cikin wadannan hukumomin tsaron.

Majalissar Dokokin Jihar Katsina Ta Nemi A Ɗauki Matakan Gaggawa Kan Matsalar Tsaro A Matazu Da Sabuwa

  Majalisar Dokokin Jihar Katsina ta yi kira ga Gwamnatin Jiha da ta Tarayya da su ɗauki matakan gaggawa kan ƙara ta’azzarar matsalar tsaro a Matazu, Sabuwa da wasu yankuna. A zaman majalisar na ranar Litinin 11/08/2025, ƙarƙashin jagorancin Rt. Hon. Nasir Yahaya Daura, Majalisar ta amince da ƙudurin ƙara yawan jami’an tsaro, musamman a Tashar Bawa da sauran wuraren da ke fama da hare-haren ‘yan bindiga. Ƙudurin ya fito ne daga Hon. Ibrahim Umar Dikko na Matazu da Hon. Ibrahim Danjuma Machika na Sabuwa, inda suka nuna damuwa kan kashe-kashe, barin gidaje da hana manoma noma sakamakon harin  ƴan fashin Daji. Sun kuma nuna damuwa da janyewar jami’an tsaro daga wasu ƙauyuka. ‘Yan majalisa daga wasu mazaɓu sun goyi bayan ƙudurin tare da buƙatar a dawo da jami’an tsaro da inganta haɗin gwiwa don dawo da zaman lafiya. Shugaban Majalisar ya jaddada buƙatar ɗaukar matakan gaggawa don kare rayuka da dukiyoyi a duk faɗin jihar.