Rundunar Yan Sanda Ta Jihar Katsina a karkashin jagorancin Kwamishina Bello Shehu ta samu nasarar kama masu laifuka daban-daban har su 302 a cikin Watan Juli na wannan shekarar da muke ciki.
Kakakin Rundunar DSP Abubakar Sadiq Aliyu ne ya tabbatar da hakan ga Manema Labarai a Hedikwatar Rundunar da ke Katsina,kuma Accuracy News Hausa ta shaida.
Kamar yadda ya bayyana,masu aikata laifukan da aka kama sun hada da wadanda ake zargi da aikata laifin fashi da makami su 14 da wadanda ake zargi da aikata laifin kisan kai su 22 sai masu laifin fyade su 25.
Haka zalika,Rundunar ta chafke wadanda ake zargi da aikata laifin satar kayan Gwamnati su 20 da masu laifin yadara su 2 da masu laifin safara da sayar da miyagun kwayoyi su 26.
Bugu da kari,akwai masu aikata laifuk daban-daban har su 194,wadanda ba'a ambata ba a cikin wancan rukunin na masu aikata laifukan.
Baya ga wannan, rundunar ta kuma samu nasarar kwato dabbobi 199 da ɓarayin shanu suka sata,sai kuma mutane sama da 50 da aka samu nasarar cetowa daga masu garkuwa da mutane.
Kayayyakin da aka samu daga wadanda ake zargin sun hada da mashina 2 da aka sata da motoci 3 sai kuma tulin miyagun kwayoyi da dai sauran su.
Accuracy News Hausa ta tsinkayi Kakakin Rundunar DSP Abubakar Sadiq yana mai danganta nasarorin bisa ga jajircewar jami'an rundunar,bisa ga hadin kai da suke samu daga Kwamishina Bello Shehu.
Ya kuma yabawa Gwamnatin Jihar Katsina da al'ummar Jihar,bisa ga goyon baya da hadin kai da suke baiwa rundunar,sai ya yi rokon karin hakan.
Daga karshe ya yi kira ga al'ummar Jihar Katsina akan koda yaushe su rika sanar da Ofishin Yan Sanda mafi kusa duk wani abinda basu aminta da shi ba,domin daukar matakin da ya kamata.
Za'a Iya Kiran Lambobin Waya Kamar Haka,Domin Samun Daukin Rundunar:
*0815697777722
*0902220969033
*07072722539

Comments
Post a Comment